Jakadan Brazil A Siriya Ya Koma Bakin Aikinsa A Birnin Damascas.
Jakadan kasar Brazil a kasar Siriya ya koma bakin aikinsa bayan shekaru kimani 7 da barin kasar.
Kamfanin dillancin labaran gwamnatin kasar Siriya SANA ya bayyana cewa Jakadan kasar Brazil a kasar Siriya ya mika takardun komawa bakin aikinsa ga ministan harkokin wajen kasar Siriya Walidul Mu'allim.
Labarin ya kara da cewa Fabiu-Fas Bitoluca ya bar birnin Damascas ne a shekara 2012 saboda matsalolin tsaro, amma duk tare da haka kasar Brazil ta bar karamin ofishin jakadancin kasar tana aiki a birnin Damascus a duk tsawon wannan lokaci.
A wannan karon dai jakadan kasar ta Brazil a Siriya ya ce gwamnatinsa tana son zuba jari a shirin gwamnatin kasar na sake gina kasar.
Kafin haka dai ita ma gwamnatin kasar ta siriya ta bukaci sake dawo da huldan tattalin arziki na kasar ta Brazil a cikin watan Jenerun shekra ta 2018 da ta gabata.
Ya zuwa yanzu dai mafi yawan kasashen Larabawa da kuma kasashen Turai sun sake bude ofisoshin jakadancinsu a birnin Damascas, bayan an sami zaman lafiya a birnin da ma mafi yawan yankunan kasar.