Mar 03, 2019 12:32 UTC
  • Siriya Ta Zargi Amurka Da Yin Amfani Da Sinadarai Masu Guba A Gabashin Kasar

Kasar Siriya ta zargi kawacen da Amurka ke jagoranta da yin amfani da sinadarai masu guba a yankin gabashin kasar.

Kamfanin dillancin labaran Siriya na SANAA ya ce kawacen da Amurka ke jagoranta ya yi amfani da sinadarai masu guba a yankin da kungiyar (IS) ke rike da shi a gabashin kasar.

An kaddamar da harin ne kan wasu gonaki dake garin Baghouz, wanda shi ne kadai yankin da ya rage a hannun kungiyar ta (IS) a gabashin tekun Euphrates dake gabashin lardin Deir al-Zour, saidai ba'a bayyana cikakken rahoton hasarar rayuka ba a sanadiyyar harin.

A wani labari kuma, dakaru da Amurka ke jagoranta sun fara kaddamar da wasu hare hare na karshe kan matattarar mayakan kungiyar ta (IS) a yankin na Baghouz.

A halin da ake ciki dai yanki daya tilo da ya rage a hannun mayakan 'yan ta'addan na (IS) shi ne garin Baghouz.

Tags