Pars Today
Wani dan majalisar dokokin kasar ta Iraki, Muhammad al-Baldawi ne ya yi gargadin cewa; Amurka tana kokarin sakin fursunonin 'yan ta'adda a cikin Iraki domin sake ba su damar farfadowa
Gwamnatin kasar Switzerland ta bakin ministan sharia na kasar ta bukaci a gurfanar da yan asalin kasar wadanda aka kama a cikin mayakan kungiyar Daesh a kasashen Siriya da Iraqi, a kasashen biyu.
Ma'aikatar cikin gida na kasar Morocco ta bada sanarwan cewa ta sami nasarar wargaza wani shirin hare0haren ta'addanci a yammacin kasar.
Majiyar shari'a a kasar Rasha ta bada sanarwan cewa an yanke hukunci na zaman kaso mai tsawo ga wasu yayan kungiyan yan ta'adda ta Daesh su biyar.
Sojojin kasar Amurka 4 ne suka halaka a yau a garin manbij na kasar Syria, yayin da wasu uku suka samu munanan raunuka, bayan wani harin bam da aka kai musu.
Ma'aikatar harkokin cikin gidan kasar ta Moroko ce ta sanar da rusa wata kungiya a arewacin kasar wacce take da alaka da kungiyar Da'esh
Yansanda a kasar Morocco sun bada sanarwan kama mutane ukku wadanda ake tuhuma da kashe wasu mata biyu yan yankin Scandanvia yan yawon shakatawa a cikin kasar.
Kungiyar kare hakkin bil'adama ta "Human Right Watch" ta sanar da cewa kungiyar "Da'esh" ta kashe fursunoni 700 a gabacin kasar Syria a cikin watanni biyu da su ka gabata
A yau ne ake gudanar da gudanar da bukukuwan cika shekara guda da murkushe kungiyar 'yan ta'addan Daesh a fadin kasar Iraki.
Kafafen watsa labarun kasar Libya sun sanar da cewa kungiyar 'yan ta'adda da Da'esh ta kai hari akan wani ofishin 'yan sanda da ke yankin kudu masu gabacin kasar