Iraki Ta Gargadi Amurka Akan Kokarin Sake Farfado Da ISiS
(last modified Thu, 21 Feb 2019 12:27:44 GMT )
Feb 21, 2019 12:27 UTC
  • Iraki Ta Gargadi Amurka Akan Kokarin Sake Farfado Da ISiS

Wani dan majalisar dokokin kasar ta Iraki, Muhammad al-Baldawi ne ya yi gargadin cewa; Amurka tana kokarin sakin fursunonin 'yan ta'adda a cikin Iraki domin sake ba su damar farfadowa

Muhammad al-Baldawi ya nuna dawumarsa akan yadda Amurkan take son maimaita abin da ya faru a gidajen kurkukun Abu Guraib, al-Tasfirat, da Takrit.

Dan majalisar Irakin ya yi ishara da yadda Amurka ta fusata saboda Irakawa sun yi yarda su ba ta damar kafa sansanin soja a kasar, sannan ya kara da cewa; Da akwai 'yan ta'adda masu yawa a cikin gidajen kurkukun Iraki wadanda aka fitar da su domin samar da gibi na tsaro a kasar.

A gefe daya, wani kwamanda na rundunar sa kai ta Hashdus-Sha'abi Qasim Muslih ya ce; Amurkan ta yi wa 'yan ta'adda ishara akan su sake farfado da ayyukansu na ta'addanci