Bukukuwan Cika Shekara Guda da Murkushe Daesh A Iraki
(last modified Mon, 10 Dec 2018 05:10:09 GMT )
Dec 10, 2018 05:10 UTC
  • Bukukuwan Cika Shekara Guda da Murkushe Daesh A Iraki

A yau ne ake gudanar da gudanar da bukukuwan cika shekara guda da murkushe kungiyar 'yan ta'addan Daesh a fadin kasar Iraki.

Kamfanin dillancin labarai na Saumaria News ya bayar da rahoton cewa, gwamantin kasar ta sanar a  hukumance kan cewa, a Litinin a dukkanin fadin kasar za a gudanar da bukukuwan cika shekara guda da murkushe kungiyar 'yan ta'addan wahabiyawa ta Daesh tare da kammala dawo da dukkanin yankunan da kungiyar ta kwace iko da su a lokutan baya a cikin kasar ta Iraki.

An sanar da ranar ta yau a matsayin ranar hutu a hukumance a kasar Iraki, haka nan kuma Firayi ministan kasar ta Iraki Adel Abdulmahdi zai gabatar da jawabi ga al'ummar kasar, wanda dukkanin gidajen talabijin da radiyo na kasar za su watsa, bayan nan kuma za a girmama iyalan wadanda suka rasa rayukansu sakamakon ta'addancin Daesh a kasar, kamar yadda kuma za a daga tutocin Irakia  dukkanin sassan kasar, da hakan ya hada da gidajen jama'a da wuraren kasuwanci da tituna da kan ababen hawa.