Pars Today
Kungiyar taliban ta dauki alhakin kai wani hari da yayi sanadin mutuwar mutum 65, a wata cibiyar horon jami'an leken asiri dake lardin Wardak a kudancin kasar ta Afganistan.
Kungiyar Taliban ta dauki alhakin kai harin bam din da ya hallaka wasu sojin Amurka uku a birnin Ghazni dake tsakiyar kasar Afganistan.
Manzon musamman na Amurka da ke shiga tsakani a tattaunar sulhu da kungiyar Taliban, ya kasa shawo kan mayakan kungiyar kan su rungumi tafarkin zaman lafiya.
Rahotanni daga Afganistan na cewa kwamandan kungiyar tsaro ta NATO, Janar din sojin Amurka, Scott Miller, ya tsallake rijiya da baya a wani harin bindiga da kungiyar taliban ta dauki alhakin kaiwa a yankin Kandahar.
Ministan harakokin wajen kasar Rasha ya tabbatar da cewa kungiyar Taliban za ta haslarci zaman da za a yi game da rikicin kasar Afganistan a birnin Moscow.
Kungiyar Taliban a Afganistan ta yi watsi da kiran shugaban kasar, Ashraf Ghani, na tsawaita tsagaita wuta a dalilin karshen watan Ramadan.
Ma'aikatar tsaron kasar Afghanistan ta sanar da cewa an hallaka shugaban kungiyar Taliban na kasar Pakistan Mullah Fazlullah a wani harin da aka sojojin Amurka da na Afghanistan suka kai masa ta sama a kan iyakan kasashen kasar ta Pakistan da Afghanistan.
Kungiyar 'yan ta'adda ta taliban ta sanar da tsagaita buda wuta tsakaninta da sojojin Afganistan, a karshen watan Ramadan, wanda kuma shi ne irinsa na farko a cikin shekaru 17 bayan da sojojin kasashen ketare karkashin jagorancin Amurka suka kawar da mulkin daga hannun 'yan taliban din.
Hukumomi a birnin Kabul na kasar Afganistan sun sanar da cewa adadin mutanan da suka rasa rayukansu a harin kunar bakin wake da wani da wani dan ta'addar ISIS ya kai ya haura zuwa 48 tare da jikkata wasu sama da 100 na daban
Kungiyar Taliban a Afganistan ta yi fatali da tayin gwamnatin kasar na bude tattaunawar zaman lafiya tsakaninsu.