Pars Today
Kakakin Majalisar Dinkin Duniya ne ya bayyana cewa; sabbin tashe-tashen hankulan da suke faruwa a cikin yankin arewa maso gabashin Najeriya sun sa dubban mazauna yankin yin gudun hijira
Rahotanni da suke fitowa daga birnin Khartum sun ce masu Zanga-zangar sun tasamma fadar shugaban kasar suna masu yin kira a gare shi da ya yi murabus
Jami'an 'yan sanda na kasar Habasha sun sanar da mutuwar mutum 23 sanadiyar rikicin kabilanci cikin wannan mako a kasar
Cikin Wani Rahoto da ta fitar a Wannan alhamis, Hukumar Ilimi da Raya Al'adu ta MDD Unesco, muzgunawa da cin mutunci ya lalata karatun matasa 'yan shekaru 13 zuwa 15 kimanin miliyan 150 a Duniya
Wani mutum dauke da wuka ya farma matafiya a cikin wata motar bus a yankin arewacin garin Luebeck da ke kasar Jamus, inda ya jikkata matafiya 14 a jiya Juma'a.
Zanga - zangar nuna kin jinin gwamnatin kasar Nicaragua ta lashe rayukan mutane akalla 98 tare da jikkata wasu adadi mai yawa.
Za a gudanar da wani taron karawa juna sani harkokin kudi a mahangar addinin musulunci a kasar Ghana.
Zanga-zangar nuna adawa da gwamnatin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo ta baya -bayan nan ta rikide zuwa tarzoma a birnin Kinshasa fadar mulkin kasar lamarin da janyo hasarar rayukan mutane da jikkatan wasu adadi na daban.
Tashe-tashen hankula na nuna kiyayya ga gwamnatin kasar Guinea Konakri ya kai ga kisan dansanda guda da kuma raunata mutane da dama.
Shugaban kasar Togo, Faure Gnassingbé, ya zargin masu adawa da gwamnatinsa da cewa suna kokarin tada da zaune tsaye a kasar