-
Zarif: Iran Za Ta Ci Gaba Da Shirinta Na Nukiliya, Matukar Amurka Ta Fice Daga Yarjejeniyar Nukiliya
Apr 21, 2018 05:44Ministan harkokin wajen kasar Iran, Dakta Muhammad Jawad Zarif, ya bayyana cewa Iran za ta sake dawowa da ci gaba da ayyukanta na nukiliya matukar dai shugaban Amurka ya sanar da ficewar Amurkan daga yarjejeniyar nukiliyan da manyan kasashen duniya suka cimma da Iran din.
-
Iran Ta Gindaya Sharadi Kafin Tattaunawa Kan Shirinta Na Makamai Masu Linzami
Mar 03, 2018 15:53Iran ta ce sharadin bude tattaunawa kan shirinta na makamai masu linzami, zai soma ne idan Amurka da Turai suka lalata makamman nukiliya da da masu cin dogon zango na Amurka da na Turai.
-
Araqchi: Iran Za Ta Fice Daga Yarjejeniyar Nukiliya Idan Ya Zamana Babu Amfanin Da Take Samu
Feb 22, 2018 17:40Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta bayyana cewar za ta fice daga yarjejeniyar nukiliya matukar dai ya zamana ba ta amfanuwa da wani abu daga cikin abin da aka cimma sakamakon barazanar da Amurka take ci gaba da yi wa kamfanoni da cibiyoyin musayen kudade da suke son mu'amala da ita.
-
Iran Ba Za Ta Bari A Binciki Sansanonin Sojinta Ba, Don Ba Ya Cikin Yarjejeniyar Nukiliya
Jan 15, 2018 05:51Kakakin hukumar kula da makamashin nukiliya na kasar Iran, Behrouz Kamalvandi, ya bayyana cewar Iran ba za ta taba bari masu binciken kasa da kasa su kai ziyarar bincike sansanonin sojin kasar ba.
-
Iran Ba Za Ta Girmama Wani Abu Sama Da Abin Da Aka Cimma A Yarjejeniyar Nukiliya Ba
Jan 13, 2018 17:06Ma'aikatar harkokin wajen kasar Iran ta bayyana cewar Jamhuriyar Musulunci ta Iran ba za ta girmama duk wani abu sama da abin da aka cimma a yarjejeniyar nukiliyar da ta cimma da manyan kasashen duniya a shekara ta 2015 ba.
-
Zarif: Iran Za Ta Ci Gaba Da Riko Da Yajejeniyar Nukiliya Ne Idan Amurka Ta Girmama Ta
Jan 11, 2018 05:48Ministan harkokin wajen kasar Iran Dakta Muhammad Jawad Zarif ya bayyana cewar Jamhuriyar Musulunci ta Iran za ta ci gaba da girmama yarjejeniyar nukiliyan da aka cimma da ita ne matukar dai Amurka ta ci gaba da girmama yarjejeniyar ba tare da yi mata karan tsaye ba.
-
IAEA : Iran Ta Rike Amana_ Yukiya Amano
Nov 23, 2017 17:28Babban daraktan hukumar yaki da yaduwar makamman nukiliya ta duniya (IAEA), ya ce Jamhuriya musulinci ta Iran ta rike amana kan yarjejeniyar nukiliyar da manyan kasashen duniya suka cimma da ita a 2015.
-
Shugabannin Rasha da Faransa Sun Tabbatar Da Ci Gaba Da Girmama Yarjejeniyar Nukiliyar Iran
Nov 03, 2017 05:53Shugabannin kasashen Rasha, Vladimir Putin da Faransa Emmanuel Macron sun sake tabbatar da aniyarsu ta ci gaba da girmama yarjejeniyar nukiliyan da aka cimma da kasar Iran bugu da kari kan wajibcin ci gaba da aiwatar da ita.
-
Amano: Iran Tana Ci Gaba Da Aiwatar Da Yarjejeniyar Nukiliya Kamar Yadda Aka Cimma
Oct 30, 2017 05:50Shugaban hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya (IAEA) Yukiyo Amano ya bayyana cewa Iran tana ci gaba da aiwatar da yarjejeniyar nukiliya kamar yadda aka cimma da ita a shekara ta 2015.
-
Rasha: Duk Wani Sauyi Cikin Yarjejeniyar Shirin Iran Na Nukiliya Na Iya Kawo Karshenta
Oct 22, 2017 05:20Kasar Rasha ta bayyana cewar ba ta da wani shakku cikin cewa Iran tana ci gaba da aiwatar da dukkanin abubuwan da aka cimma da ita cikin yarjejeniyar nukiliya, tana mai cewa yin sauyi cikin yarjejeniyar yana iya kawo karshenta.