Iran Ta Gindaya Sharadi Kafin Tattaunawa Kan Shirinta Na Makamai Masu Linzami
(last modified Sat, 03 Mar 2018 15:53:20 GMT )
Mar 03, 2018 15:53 UTC
  • Iran Ta Gindaya Sharadi Kafin Tattaunawa Kan Shirinta Na Makamai Masu Linzami

Iran ta ce sharadin bude tattaunawa kan shirinta na makamai masu linzami, zai soma ne idan Amurka da Turai suka lalata makamman nukiliya da da masu cin dogon zango na Amurka da na Turai.

Da yake bayyana wannan sharadin, kakakin rundinar sojin Iran, Birgediya Janar, Seyyed Massoud Jazayeri, ya ce kufan bakin da Amurka ta ke kan takaita shirin Iran na makamai masu linzami, yana nuna karara gazawar Amurka wajen cimma manufofinta a yankin.

A cewarsa karfin da Iran take da shi kan makamman na kariya da ya dogara da tsoma bakin kasashen waye da Iran bata kai matsayin da take a yanzu ba.  

Wannan dai na zuwa ne a yayin da ministan harkokin wajen Faransa, Jean Yves Le Drian, ke shirin kawo ziyara a Iran a ranar Litini mai zuwa.

Faransa dai na daga cikin kasashen Turai dake neman a tattauna kan shirin Iran na makamai masu Linzami bisa bukatar Amurka, batun da Iran din ta ce ko da wasa baya daga cikin batutuwan da za'a tattauna don babu wata kasar Turai da zata amince yi mata irin hakan kan sha'anin tsaronta.