Pars Today
Kakakin ma'aiktar harkokin wajen kasar Iran ya bukaci kasashen Turai su sauke nauyin da ya hau kansu dangane da yerjejeniyar shirin Nkliyar kasar Iran .
Shugaban kasar Sudan ta kudu Salva Kiir, ya zargi masu bada taimako na kasashen yammacin duniya da gazawa wajen kin samar da kudaden da za'a yi amfani da su wajen aiwatar da yarjejeniyar zaman lafiya wanda zai kawo karshen yakin basasar kasar da aka shafe sama da shekaru biyar anayi a kasar.
Mukadashin kwamandan rundinar kare juyin juya halin Musulinci na Iran, (IRGC), Birgediya Janar Salami, ya ja kunnen kasashen turai akan duk wani yunkurinsu na raba Iran da makamanta masu linzami na kare kanta.
Kungiyar tarayya ta kafa wani sabon shiri na cinikaya da Iran, wanda zai kaucewa takunkuman da Amurka ta kakaba wa Iran din bayan data fice daga yarjejeniyar nukiliya.
Tawagar masu sanya ido ta kasashen turai a zaben Najeriya, ta nuna damuwarta dangane da korar shugaban kotun kolin kasar a daidai lokacin da ya rage 'yan makwanni a gudanar da babban zaben kasar.
Kungiyar tarayya Turai (EU), da takwararta ta Afrika (AU), sun ce a shirye su ke su yi aiki da zababen shugaban kasar Jamhuriyar Demokuradiyyar Congo, Felix Tshisekedi.
Iran ta mayar wa da kasashen turai martani kan kakaba mata da sabbin takunkumi kan zargin da kasar Danemark ta yi na alakanta wani shirin kisa ga wani mutum a cikin kasarta da tace yana da alaka da wasu jami'an leken asirin Iran.
Jagoran mabiya addinin kirista 'yan darikar Katolika na duniya Paparoma Francis, ya bukaci kasashen turai da su taimaka ma 'yan gudun hijira da suka lakahe a cikin ruwan tekun mediterranean.
Babban sakataren majalisar dinkin duniya Antonio ya nuna damuwa kan yadda ayyukan nuna kyama ga musulmi ke karuwa a duniya.
Kasar Canada, ta sanar da sanya takunkumin hana shigar kasar, ga wasu 'yan Saudiyya 17 da ake zargi da hannu a kisan dan jaridan nan Jamel Khashoggi a ranar 2 ga watan Oktoba da ya gabata a karamin ofishin jakadancin Saudiyyar na Santambul.