Feb 09, 2019 16:49 UTC
  • Sudan Ta Kudu : Kiir, Ya Zargi Kasashen Yamma Da Kawo Cikas Ga Zaman Lafiyar Kasar

Shugaban kasar Sudan ta kudu Salva Kiir, ya zargi masu bada taimako na kasashen yammacin duniya da gazawa wajen kin samar da kudaden da za'a yi amfani da su wajen aiwatar da yarjejeniyar zaman lafiya wanda zai kawo karshen yakin basasar kasar da aka shafe sama da shekaru biyar anayi a kasar.

Kiir, wanda ya bayyana hakan ga wasu manyan jami'an jam'iyya mai mulki ta Sudan (SPLM), inda ya ce, kasashen yamma da al'ummomin kasa da kasa masu samar da agajin kudade sun dauki wata irin al'ada ta "bari mu zuba ido mu gani" a matsayin wata hanyar dake kawo tsaiko wajen aiwatar da yarjejeniyar zaman lafiyar kasar wacce aka cimma matsaya kanta a watan Satumbar bara.

Sudan ta kudu ta tsunduma cikin yakin basasa ne tun a karshen shekarar 2013, tashin hankalin wanda ya haifar da karuwar 'yan gudun hijira mafi sauri a duniya.

MDD ta kiyasta kimanin mutane miliyan 4 ne daga Sudan ta kudu rikicin ya daidaita, kana ya raba su da matsugunansu inda suke neman mafaka a ciki da wajen kasar.

Da alama sabuwar yarjejeniyar zaman lafiyar da aka rattaba hannu kanta a watan Satumban bara ana samun nasarori kanta bayan da aka samu raguwar yawaitar kashe kashen rayukan jama'a a 'yan watannin da suka gabata a kasar.

Tags