-
Yan Sandan Tunusiya Suna Cikin Halin Ko Ta Kwana Domin Kalubalantar Masu Zanga-Zanga
Oct 14, 2017 19:05Rundunar 'yan sandan kasar Tunusiya tana cikin shirin ko ta kwana domin kalubalantar zanga-zangar yin Allah wadai da sojojin ruwan kasar da ake zargi da yin sanadiyyar kashe bakin haure a tekun kasar da ke lardin Kebili a tsakiyar kasar.
-
Mali: An yi Zanga-zangar Kin Jinin Ci Gaba Da Zaman Sojojin Faransa.
Oct 10, 2017 19:12Mazauna yankin Kidal da ke arewacin kasar ta Mali sun nuna kin amincewarsu da zaman sojojin Faransa a yankin.
-
Al'ummar Morocco Sun Gudanar Da Zanga-Zangar Neman Sakin Masu Rajin Kare Hakkin Bil-Adama
Oct 09, 2017 12:05Al'ummar Morocco sun gudanar da zanga-zanga a sassa daban daban na kasar musamman a birnin Casablanca cibiyar kasuwancin kasar domin neman sakin masu rajin kare hakkin bil-Adama a kasar.
-
Taron Wakilan Kasashen Afrika Da Faransa Don Bunkasa Dangantakar Bangarorin Biyu
Oct 07, 2017 06:44An kammala taron kwanaki biyu na kasashen Afrika da Faransa don bunkasa dangantaka tsakanin bangarorin biyu a fagen tattalin arziki, siyasa da kuma zamantakewa.
-
'Yan Adawa Sun Gudanar Da Gagarumar Zanga-Zangar Kin Jinin Shugaban Togo
Oct 04, 2017 17:24Rahotanni daga kasar Togo sun bayyana cewar dubun dubatan masu adawa da ci gaban mulkin shugaba Faure Gnassingbe na kasar ne suka gudanar da wata gagarumar zanga-zanga duk kuwa da barazanar da jami'an tsaron kasar suka yi musu na daukar mataki a kansu.
-
Daruruwan Mata A Mali Sun Gudanar Da Zanga-Zangar Neman Ficewar Sojojin Faransa Daga Kasar
Oct 03, 2017 18:59Mata a garin Kidel da ke arewacin kasar Mali sun gudanar da zanga-zangar lumana suna neman ficewar sojojin Faransa daga cikin kasarsu.
-
'Yan Sandan Kenya Sun Tarwatsa 'Yan Adawa Masu Zanga-Zanga A Birnin Nairobi
Oct 02, 2017 11:23'Yan sandan kasar Kenya sun yi amfani da borkonon tsohuwa wajen tarwatsa 'yan adawa masu gudanar da zanga-zanga a babban birnin kasar, Nairobi, wadanda suka fito don bukatar da a sallami jami'an hukumar zaben kasar da suka gudanar da zaben shugaban kasar da aka soke.
-
'Yan Sanda Da Masu Zanga-Zangar Kyamar Rashawa Sun Yi Taho Mu Gama A Zambiya
Oct 01, 2017 10:23'Yan sanda a kasar Zambiya sun far ma masu zanga-zangar kin jinin rashawa da cin hanci da suka taru a gaban majalisar dokokin kasar a daidai lokacin da ministan kudin kasar yake gabatar da kasafin kudi na shekara ga 'yan majalisar.
-
Al'ummar Gabashin Kasar DR Congo Sun Gudanar Da Zanga-Zanga Kan Rashin Tsaro A Yankinsu
Sep 27, 2017 03:03Al'ummar garin Bukavu da ke lardin Kivu ta Kudu a shiyar gabashin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo sun gudanar da zanga-zanga domin nuna rashin amincewarsu da ci gaba da bullar tabarbarewan matakan tsaro a yankin.
-
Za'a Gudanar da Zanga-Zanga A Libya Don Nuna Damuwa Da Irin Halin Da Kasar Take Ciki
Sep 24, 2017 11:49Wani tsohon dan takarar neman kujerar Priminista a kasar Libya ya bukaci mutanen kasar su fito don gudanar da zanga-zanga a duk fadin kasar don nuna rashin amincewarsu da halin tattalin arziki da siyasar kasar suke tafiya.