Pars Today
Ministan harkokin wajen kasar Iran ya gudanar da zaman tattaunawa na musamman da manyan jami'an Majalisar Dinkin Duniya kan matsalolin kasashen Myanmar, Yamen da Siriya.
A jiya litinin ne dai ministan harkokin wajen na Iran Muhammad Jawad Zarif da takwaransa na Turkiya Maulud Jawush Uglu suka yi magana akan yadda za a tsaida kisan da ake yi wa musulmi Rohingha na kasar Myanmar.
Ministan harkokin wajen JMI Mohammad Jawad Zareef ya bukaci kasashen musulmi da sauran kasashen duniya su dauki mataki a aikace kan musibar da musulman kasar Myanmar suke ciki .
Ministan harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa: An kama hanyar kawo karshen kungiyoyin 'yan ta'adda a kasar Siriya, kuma bayan kawo karshen ayyukan ta'addanci a Siriya al'ummar kasar ne kadai suke da hakkin tantance makomar kasar ta Siriya da kansu.
Jakadun kasashen Mali, Nigeria, Sirilanka da Kuma Jumhuriyar Check sun gana da ministan harkokin wajen kasar Iran Mohammad Jawada Zarif
Ministan harkokin wajen kasar Iran ya jaddada cewa: Manufar Jamhuriyar Musulunci ta Iran ita ce kare yarjejeniyar makamashin nukiliyar da aka cimma tsakaninta da manyan kasashen duniya gami da kalubalantar bakar siyasar Amurka.
Ministan harkokin wajen kasar Iran Dakta Muhammad Jawad Zarif ya bayyana cewar babu ruwan Musulunci da ayyukan ta'addancin da ake aikatawa da sunansa.
Ministan harkokin wajen kasar Iran Muhammad Jawad zarif ya bayyana cewa, yana fatan zaman da kasashen msuulmi suka gudanar a birnin Istanbul na kasar Turkiya Palastinu ya haifar da da mai ido.
Ministan harkokin wajen kasar Iran Muhammad jawad zarif ya bayyana cewa, mayar da yankin gabas ta tsakiya wata kasuwar sayar da makamai, ba zai haifar ma yankin da mai ido ba.
A ci gaba da gudanar da ziyarar aiki da yake yi a wasu daga cikin kasashen arewacin Afirka, ministan harkokin wajen Iran Muhammad Jawad zarif ya isa kasar Mauritania a yau, inda ya gana da manyan jami'an gwamnatin kasar.