Shugaban Mauritania Ya Gana Da Ministan Harkokin wajen Iran A Nouakchott
A ci gaba da gudanar da ziyarar aiki da yake yi a wasu daga cikin kasashen arewacin Afirka, ministan harkokin wajen Iran Muhammad Jawad zarif ya isa kasar Mauritania a yau, inda ya gana da manyan jami'an gwamnatin kasar.
Kamfanin dillancin labaran IRNA ya bayar da rahoton cewa, Zarif ya gana da takwaransa na Mauriya Isselkou Wuld Ahmad a yau a birnin Nouakchott, daga nan kuma ya gana da shugaban kasar ta Mauritania Muhamamd Wuld Abdulaziz, inda suka tattauna muhimamn batutuwa da suka shafi karfafa alaka tsakanin kasashen biyu.
Zarif ya bayyana cewa sun tattauna tare da jami'an Mauritani a akan batun bunkasa alakar tattalin arziki tsakanin Iran da Mauritania, da kuma batutuwa na siyasa, musamman halin da ake ciki a yankin gabas ta tsakiya, inda dukaknin bangarororin suka jaddada wajabcin warware matsalolin da ake fama da su ta hanyar tattaunawa.