Ministan Harkokin Wajen Iran Zai Ziyarci Kasar Syria
Ma’aikatar harkokin wajen Jamhuriyar musulunci ta Iran ta sanar da cewa; ministan harkokin wajen kasar Muhammad Jawad Zarif zai kai ziyara kasar Syria inda zai gana da shugaba Basshar Assad.
A wata hira da tashar talabijin din Al-Furat ta yi hira da shi, Zarfi ya ce zai je Syria ne bisa gayyatar da shugaban kasar Basshar Assad ya yi masa.
Bugu da kari tashar talabijin din ta ba da labarin cewa; shi ma shugaban kasar Iran Dr. Hassan Rauhani zai ziyarci kasar ta Syria a nan gaba kadan.
A makon da ya wuce ne dai shugaban kasar Syria Basshar Assad ya kawo ziyara Iran in da ya gana da manyan jami’an kasar da su ka hada shugaban kasa da kuma jagoran juyin musulunci Ayatullah Sayydi Ali khamnei.