Pars Today
Babbar jam'iyyar adawa ta Zimbabuwe MDC, ta bayyana cewa za ta fitar da wata sanarwa kan matakin da za ta dauka na kalubalantar sakamakon zaben shugaban kasar da aka gudanar a makon da ya gabata a gaban kuliya.
Shugaban kasar Zimbabwe Emmerson Mnangagwa, bayan ya sami nasara a zaben shugaban kasar da aka gudanar a yan kwanakin da suka gabata a bukaci mutanen kasar da magoya bayansa da kuma yan adawa su zo su hada kai da shi don kawo ci gaba a kasar.
Jagoran 'yan adawa a Zimbabwe, Nelson Chamisa, ya yi wasti da sakamakon zaben shugaban kasar da hukumar zaben kasar ta sanar.
Babban magatakardar Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya bayyana damuwarsa akan rikicin da ya kunno kai bayan zaben shugaban kasa a Zimbabwe yana kiran al'ummar kasar da su kai zuciya nesa.
Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres, ya bukaci bangarorin siyasar Zimbabwe da su kai zuciya nesa, biyo bayan tarzomar da ta barke a kasar saboda zargin magudin zabe.
Hukumar zaben kasar Zimbabwe ta sanar da cewa: Jam'iyyar Zanu-PF mai mulki a kasar ita ce ta samu mafi yawan kujerun 'yan Majalisun Dokokin Kasar a zaben da aka gudanar a ranar Litinin da ta gabata.
Dubban magoya bayan jam'iyyar adawa mafi girma a kasar Zimbabwe sun fito zanga zanga a birnin Harare babban birnin kasar inda suke nuna rashin amincewarsu da sakamakon zaben majaliasar dokokin wasar wanda ya nuna cewa jam'iyya mai mulki ce ta sami nasara a cikinsa.
Sakamakon farko-farko na zaben da aka gudanar a Zimbabwe yana nuni da cewa: Jam'iyya mai mulki ta Zanu-PF ce ta lashe mafi yawan kujerun 'yan Majalisun Dokokin Kasar.
'Yan hammaya a Zimbabwe, sun fara ikirarin lashe zaben shugaban kasar da aka kada kuri'arsa a jiya Litini.