Shugaban Kasar Zimbabwe Ya Bukaci Hadin Kan Mutanen Kasarsa
Shugaban kasar Zimbabwe Emmerson Mnangagwa, bayan ya sami nasara a zaben shugaban kasar da aka gudanar a yan kwanakin da suka gabata a bukaci mutanen kasar da magoya bayansa da kuma yan adawa su zo su hada kai da shi don kawo ci gaba a kasar.
Kamfanin dillancin labaran Reuters ya nakalto Emmerson Mnangagwa yana fadar haka ne a shafinsa na "Tweeter" a yau Asabar.
A jiya jumma'a ne hukumar zaben kasar Zimbabwe ta bada sakamakon zaben shugaban kasa na kashe, inda shugaban kasa mai ci Emmerson Mnangagwa ya sami kashi 50.8% na yawan kuri'in da aka kada a yayinsa babbar abokin adawarsa Nelson Chamisa ya tashi da kashi 44% na yawan kuri'un da aka kada.
Bayan sanarda sakamakon zaben ne yan adawa suka fito zanga zanga wanda ya kai ga mutuwar mutane akalla 6 bayan da yan sanda suka yi kokarin tarwatsa su.