Pars Today
Rahotanni daga Afganistan na cewa mutane 25 ne suka mutu a wani hatsarin jirgin sama mai saukar ungulu na soji a yammacin kasar.
Kakakin ma'aikatar harakokin wajen Iran ya taya al'ummar kasar Afganistan murnar zaben 'yan majalisa a kasar, sannan ya ce wannan babban sauyi ne aka samu a bangaren tsaro da kuma ci gaban kasar.
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Iran ya taya gwamnatin Afganistan da al'ummar kasar murnar samun nasarar gudanar da zaben 'yan Majalisun Dokoki a kasar.
Akalla mutane 15 ne suka rasa rayukansu sanadiyyar harin kunan bakin wake wanda aka kai kan wata mazaba a birnin Kabul babban birnin kasar Afaganistan a jiya Asabar.
Rahotanni daga Afganistan na cewa an samu tashin bama-bamai a sassan daban na Kabul babban birnin kasar a daidai lokacinda al'ummar kasar suka fara kada kuri'a a zaben 'yan majalsuar dokoki a yau Asabar.
A jiya ne kungiyar Taliban ta kaddamar da wani hari a cikin jahar Qandahar ta kasar Afghanistan, wanda kungiyar ta ce ta yi nufin halaka babban kwamandan sojojin NATO da ke kasar Afghanistan ne, wanda kuma ya tsallake rijiya da baya.
Rahotanni daga Afganistan na cewa kwamandan kungiyar tsaro ta NATO, Janar din sojin Amurka, Scott Miller, ya tsallake rijiya da baya a wani harin bindiga da kungiyar taliban ta dauki alhakin kaiwa a yankin Kandahar.
Rahotanni daga Afganistan na cewa wani harin kunar bakin wake ya yi ajalin mutum 8, da kuma raunana wasu 11, a wani ofishin dan takara zaben 'yan majalisar dokoki a garin Lashkar Gah dake yankin Helmand a kudancin kasar.
Rahotannin daga Afganistan na cewa mutane akalla bakwai ne suka rasa rayukansu a lokacin da wani dan kunar bakin wake ya tarwatsa kansa a wani wurin gangamin zabe a gabshin kasar.
Ma'aikatar harkokin wajen kasar Rasha ta gabatar da goron gayyata ga Jamhuriyar Musulunci ta Iran kan halartar zaman taron neman wanzar da zaman lafiya da sulhu a kasar Afganistan.