-
Afrika Ta Kudu : Jacob Zuma, Ya Yi Murabus
Feb 15, 2018 05:52Shugaban Afrika ta Kudu, Jacob Zuma, ya sanar da yin murabus daga mulkin kasar, bayan shafe makwanni yana fuskantar matsin lamba daga jam'iyyarsa ta ANC.
-
Wa'adin Sa'oi 48 Ga Shugaba Zuma Da Ya Sauka Daga Karagar Mulkin Afirka Ta Kudu
Feb 14, 2018 05:57A ci gaba da rikicin siyasa da ya kunno kai a kasar Afirka ta Kudu, jam'iyyar ANC mai mulki a kasar, a wani zama da ta gudanar a jiya Talata karkashin jagorancin shugabanta Cyril Ramaphosa, ta ba wa shugaban kasar Jacob Zuma wa'adin sa'oi 48 da yayi murabus daga karagar mulki ko kuma a fara shirin tsige shi.
-
Afrika Ta Kudu : Zuma Zai Bayyana Matsayinsa Ranar Laraba
Feb 13, 2018 16:25Wasu majiyoyi daga AFrika ta Kudu na cewa, shugaban kasar Jacob Zuma dake fusknatr matsin lamba zai bayyana matsayinsa a gobe Laraba.
-
Afirka Ta Kudu: ANC Ta Bayar Da Wa'adin Sa'oi 48 Ga Zuma Da Ya Yi Murabus
Feb 13, 2018 06:35Jam'iyyar ANC mai mulki a kasar Afirka ta kudu ta bayar da wa'adin kwanaki biyu ga shugaba Jacob Zuma da ya yi murabus daga mukaminsa na shugaban kasar, ko kuma a tsige shi.
-
Fadar Shugaban Afirka Ta Kudu Ta Musanta Labarin Cewa Shugaba Zuma Zai Yi Murabus
Feb 12, 2018 17:58Fadar shugaban kasar Afirka ta Kudu ta bayyana labaran da suke cewa shugaban kasar Jacob Zuma ya amince yayi murabus daga karagar mulkin kasar tana mai bayyana labarin da cewa 'zuki ta malle' ne.
-
Rikicin Siyasar Afirka Ta Kudu, Alamu Na Nuna Karshen Mulkin Zuma Ya Gabato
Feb 08, 2018 05:55Shugaban jam'iyyar ANC mai mulki a Afirka ta Kudu kana kuma mataimakin shugaban kasar Cyril Ramaphosa ya sanar da cewa yana nan yana ci gaba da tattaunawa da shugaba Jacob Zuma dangane da yadda zai yi murabus da mika mulki, wata babbar alama da ke nuna cewa daga dukkan alamu mulkin shugaba Zuman ya zo karshe bayan shekara da shekaru na matsaloli da badakala kala-kala.
-
Shugaban Jam'iyya Mai Mulki A Afrika Ta Kudu Ya Ce Zai Sanar Da Makomar Shugaban Kasar A Nan Gaba
Feb 07, 2018 19:02Shugaban jam'iyyar ANC mai mulki a kasar Afrika ta Kudu ya bayyana cewa: A cikin 'yan kwanaki masu zuwa zai sanar da makomar shugaban kasar Jacob Zuma da yake fuskantar matsin lamba kan yin murabus daga kan mukaminsa.
-
Shugaban Kasar Afirka Ta Kudu Ya Amince Da Yi Murabus
Feb 07, 2018 12:30Kafafen watsa labarun kasar Afirka Ta Kudu ne suka ambaci cewa shugaban kasar Jacob Zuma ya aminta da yin murabus bisa sharadi
-
Afrika Ta Kudu : An Dage Jawabin Zuma Gaban Majalisa
Feb 07, 2018 05:31Majalisar Afrika ta Kudu, ta dage jawabin shekara-shekara da shugaban kasar, Jacob Zuma zai yi gabanta a ranar Alhamis, a daidai lokacin da jam'iyya ANC mai mulki ke tattauna batun tsige shi.
-
Zanga-Zangar Kin Jinin Gwamnatin Afirka Ta Kudu
Feb 06, 2018 05:38Wasu kungiyoyin fararen hula da 'yan siyasa sun gudanar da zanga-zangar neman shugaba Zuma ya yi murabus daga kan mukaminsa a daidai lokacin da jam'iyar ANC mai mulki ke gudanar da taro.