Afrika Ta Kudu : An Dage Jawabin Zuma Gaban Majalisa
(last modified Wed, 07 Feb 2018 05:31:51 GMT )
Feb 07, 2018 05:31 UTC
  • Afrika Ta Kudu : An Dage Jawabin Zuma Gaban Majalisa

Majalisar Afrika ta Kudu, ta dage jawabin shekara-shekara da shugaban kasar, Jacob Zuma zai yi gabanta a ranar Alhamis, a daidai lokacin da jam'iyya ANC mai mulki ke tattauna batun tsige shi.

Shugabar majalisar, Baleka Mbete, ta ce sun yi tunanin cewa ya kamata a samu yanayin siyasa datace kuma mai kyau a lokacin da shugaban kasar zai yi jawabi kan yanayin da kasar ke ciki.

Baynai daga kasar sun ce nan gaba za'a sanar da ranar da shugaban kasar zai yi jawabin.

Yau Laraba ne aka tsara mayan jam'iyyar ANC zasu sake haduwa kan batun na ganin Mista Zuma ya yi marabus daga mukaminsa, da kuma batun ganin an samu gwamatin wucin gadi da zata hada mambobin gwamnatinsa da kuma wanda zai gaje shi.

A nasa bangare dai, Jacob Zuma ya nemi jagororin jam'iyyar da su kara hakuri, tare da musunta zarge zargen rashawa da wasu 'ya yan jam'iyar ta ANC ke masa.