Afrika Ta kudu : An kafa Kotun Musamman Ta Yaki Da Rashawa
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i35356-afrika_ta_kudu_an_kafa_kotun_musamman_ta_yaki_da_rashawa
Shugaban kasar Afrika ta kudu Cyril Ramaphosa ya kafa wata kotun musamman ta yaki da ayyukan rashawa a kasar.
(last modified 2019-02-25T10:10:30+00:00 )
Feb 25, 2019 10:08 UTC
  • Afrika Ta kudu : An kafa Kotun Musamman Ta Yaki Da Rashawa

Shugaban kasar Afrika ta kudu Cyril Ramaphosa ya kafa wata kotun musamman ta yaki da ayyukan rashawa a kasar.

Fadar shugaban kasar ta ce, an kafa kotun ne da nufin kammala dukkan shari'un da suka jibinci cin amanar kasa wadanda ake fatan kammala su cikin gaggawa bayan kwamitocin bincike na musamman wato (SIU) sun kammala ayyukansu.

A cewar sanarwar, wadannan laifuka da kwamitin SIU ya kammala aiki kansu sun kunshi dukkan yarjejeniyoyin da aka kulla na ayyukan kwangiloli wadanda aka shirya almundahana cikinsu da kuma karya ka'ida.

Hakan yana tabbatar da cewa dukkan mutane dake da hannu wajen salwantar da kudade ko kaddarorin hukumomi za su kuka da kansu.