Ministan Cikin Gidan Afrika Ta Kudu Ya Yi Murabus
Ministan cikin gida na Afirka ta Kudu Malusi Gigaba ya ajiye mukaminsa biyo bayan cece-kucen da ake yi dangane da danganta da yake da ita da iyalan Gupta.
Malusi Gigaba wanda ya ke rike da mukamin na ministan cikin gida tun cikin watan Fabarairun wannan shekara ta 2018 da muke ciki, ya samu kansa cikin halin tsaka mai wuya bayan da ake cece-kuce kan dangantakar da yake da ita a baya da iyalan na Gupta, da kuma ake zarginsa da juya akalar gwamnatin tsohon shugaban kasar ta Afirka ta Kudu Jacob Zuma.
A baya dai Gigaba ya rike mukamin ministan kudi daga watan Maris na shekara ta 2017 da ta gabata zuwa watan Fabarairun wannan shekarar. Makwanni biyun da suka gabata dai, hukumar kula da da'ar ma'aikata ta kasar ta ce Gigaba ya saba wa kundin tsarin mulkin kasar, inda aka tuhume shi da hada kai da wani kamfani na iyalan Oppenheimer da ke da dinbin arziki.