Jan 17, 2017 17:09
Tun bayan sanar da kisan matasa 3 'yan kasar Bahrain da masarautar kasar ta yi a ranar Lahadi da ta gabata, kasar ta shiga wani hali na rashin tabbas, inda ake ci gaba da gudanar da jerin gwano da zanga-zanga a dukkanin fadin kasar, da ke la'antar masarautar kan wannan kisa da ta yi saboda dalilai na siyasa da banbancin mazhaba.