Kaddamar Da Kamfe Kan Kare Hakkokin Mata A Bahrain
Babbar cibiyar kare hakkin bil adama akasar Bahrain ta kaddamar da wani kamfe domin fallasa ayyukan cin zarafin mata da mahukuntan kasar ke yi.
Jaridar Mir'atul Bahrain ta bayar da rahoto a shafinta na yanar gizo cewa, babbar cibiyar kare hakkin bil adama a kasar Bahrain ta fitar da wani bayani a yammacin jiya, da ke cewa mahukuntan kasar suna keta hurumin bil adama a kasar, musamman ma mata daga cikinsu.
Cibiyar ta ce mahukuntan Bahrain suna sanya kafa suna yin shuri da dukkanin ka’idiji da dokoki na duniya kan hakkokin dan adam, inda sukan yi amfani da dalilai na siyasa domin cin zarafin kowa da hakan ya hada har da mata.
A cikin wannan makon ne jami’an tsaron Bahrain suka kame wasu mata guda hudu tare da cin zarafin da ke ta alfarmarsu a bainar jama’a, bisa hujjar cewa suna adawa ne da masarautar kasar.