Pars Today
Kungiyar kare hakkin bil'adamar ta kasa da kasa ta bukaci ganin kawayen kasar Bahrain sun bude baki sun taka mata birki akan keta hurumin 'yan kasar da take yi
Kungiyar kare hakkin bil adama ta kasa da kasa Amnesty International ta yi kakkausar suka dangane da hukuncin daurin rai da rai da kotun masarautar Bahrain ta yanke a kan shugaban babbar jam'iyyar adawa ta kasar Sheikh Ali Salman.
A zaman shekara-shekara na kwamitin kare hakkin bil adama na majalisar dinkin duniya da ake kammalawa yau, kasashe da dama sun nuna damuwa kan cin zarafin 'yan adam da mahukuntan Bahrain ke yi.
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Bahram Qasemi ya kirayi gwamnatin Iraki da ta hukunta wadanda suka kai hari kan karamin jakadancin Iran da ke Basara.
An saka sunan shugaban cibiyar kare hakkin bil adama a Baharain Nabil Rajab a cikin ‘yan takarar lambar kare hakkin bil adama ta kasashen turai.
An sallami babban malamin addinin muslunci na kasar Bahrain daga asibiti a birnin London, bayan jinyar da ya yi tsawon kimanin kwanaki 50, biyo bayan wani aikin tiyata da aka yi masa.
Wakilin shugaban majalisar dokokin kasar Iran kan lamuran kasa da kasa ya ce sarakunan kasar Bahrain ne suka jawo tabarbarewar lafiyar Ayatollah Isa Qasim babban malamin iddini kuma shugaban masu gwagwarmaya da neman hakkin mutanen kasar.
Shafin yanar gizo na labarai na I-24-News mallakin HKI ya bayyana cewa kasar Bahrain ce zata zama kasar Larabawa ta farko wacce zata samar da huldan jakadanci da HKI.
Kwanaki biyu ajere kenan da jami'an tsaron gwamnatin Bahrain suke kai wa gidajen fararen hula hari tare da yin barna a cikinsu
Wasu kafafen yada labarai sun bayyana cewa jakadan kasar Saudiya a kasar Masar Usama Ahmad Annaqli, da tokoransa na kasar Bahrai Rashid bin Abdurrahman Ali-khalifa sun halarci bikin cika shekaru 70 da kafuwar HKI a wani Hotel a birnin Alkahira.