Iran: Gwamnatin Bahrain Ce Ke Da Alhakin Tabarbarewar Lafiyar Ayatollah Isa Qasim
Wakilin shugaban majalisar dokokin kasar Iran kan lamuran kasa da kasa ya ce sarakunan kasar Bahrain ne suka jawo tabarbarewar lafiyar Ayatollah Isa Qasim babban malamin iddini kuma shugaban masu gwagwarmaya da neman hakkin mutanen kasar.
Kamfanin dillancin labaran Mehr na kasar Iran ya nakalto Husain Amir Abdullahiyan, mai magana da yawun Ali larijani kakkaki majalisar dokokin kasar Iran yana fadar haka a yau talata. Ya kuma kara da cewa tsare babban malamin a gidansa da kuma rashin amincewa da shawarar likitocinsa tun farko shi ya kai ga tabarbarewab lafiyar Ayatollah Isa Qasim.
A jiya litinin ne sarkin kasar Bahrain Ham Bin Isa Ali Khalifa ya bada izinin a kai Ayatollah Isa Qasim kasashen waje don jinya.
Tuni dai malamin da kuma iyalansa da wasu mukarrabansa sun isa birnin London na kasar Britania inda zai yi jinyan cututtukan da suke damunsa.
Tun shekara ta 2016 ne dai gwamnatin kasar Bahrain ta tilastawa Ayatollah Isa Qasim daurin talala a cikin gidansa a yankin Dar'a na birnin Manama babban birnin kasar Bahrain.