Pars Today
Tashar talabijin din Iraki ta bada labarin cewa; A kalla mutane 25 ne suka mutu sanadiyyar harin kunar bakin waje biyu da aka kai a birnin Bagadaza
A ci gaba da samame da sojojin gwamnatin Iraki da dakarun sa- kai na kasar ke gudanarwa a lardin Karkuk na kasar da nufin tsarkake shi daga samuwar 'yan ta'addan kungiyar Da'ish, sun yi nasarar kashe 'yan ta'adda fiye da 40.
Ministan sufuri na kasar Syria Ali Hammud ya bayyana jin dadinsa akan dawowar jirga-jirgar jirage da kuma manyan motoci a tsakanin kasarsa da Iraki.
Firaministan kasar Italiya ya gabatar da wani shiri na kwashe wani adadi na sojojin kasar sa daga kasar Iraki, domin tura su jamhuriyar Nijar domin ayyukan yaki da ta'addanci da kuma masu safarar miyagun kwayoyi a cikin watanni masu zuwa.
A ci gaba da nasarorin da ake samu a kan kungiyar ta'addancin nan ta Daesh a yankin Gabas ta tsakiya, firayi ministan kasar Iraki Haider al-Abadi ya sanar da kawo karshen kungiyar a kasar Irakin da kuma samun nasara ta gaba a kanta.
Firayi ministan kasar Iraki Haider al-Abadi ya sanar da kawo karshen yakin da gwamnatin kasar take yi da kungiyar ta'addancin nan ta Daesh a kasar bayan nasarar da dakarun kasar suka samu na kwato dukkanin yankunan da 'yan ta'addan suke rike da su a baya.
Kakakin Priministan kasar Iraqi Haidar Abadi ya bayyana jawaban shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron dangane da mayakan sha kai na kasar ta Iraqi a matsayin shishigi a cikin lamuran cikin gida na kasar.
Babban kwamandan dakarun sa kai na kasar Iraki da aka fi sani da Hashd al-Sha’abi, Hadi al-Ameri, ya bayyana cewar bayan kawo karshen kungiyar ta'addancin nan ta Daesh, wajibi ne sojojin Amurka su fice daga kasar Irakin.
A yau talata ne pira ministan kasar ta Iraki, Haydar Ibadi, ya sanar da cewa Irakin ta sami nasara akan Da'esh, amma ba zai sanar da nasarar karshe ba sai an murkushe wadanda suka gudu cikin sahara.
Kotun koli a Iraki ta sanar da soke zaben yankin Kurdistan da aka gudanar a watan Satumba da ya gabata.