Pars Today
Sojojin Iraki sun kwace lardin Rawa, na karshe dake hannun 'yan ta'adda na Da'esh.
Yau Juma'a rundinar sojin kasar Iraki ta kaddamar da farmakin kwato Rawa, lardi na karshe dake hannun 'yan ta'addan IS.
Ministocin harkokin wajen kasashen Aljeriya, Masar da Tunusiya sun yi gargadi kan hatsarin komawar 'yan ta'addan kungiyar Da'ish kasashensu da suke nahiyar arewacin Afrika.
Pira ministan kasar ta Iraki Haydar Ibadi ya jaddada cewa za su karbi iyakokin ne ba tare da tashin hankali ko amfani da karfi ba.
Gwamnan jihar Karkuk na kasar Iraki ya ce an gano wasu manyan kaburbura wadanda suke dauke da gawarwakin mutane 400 a wani wuri da ke kusa da garin Hawija, inda a nan ne aka fatattaki mayakan kungiyar IS a makon da ya gabata.
A ci gaba da farmakin da suke kan 'yan ta'adda na kungiyar IS ko Da'esh, sojojin Iraki sun yi nasara kauce ikon kauwuka da dama da suka dade karkashin kungiyar a yankin hamada dake yammacin kasar a iyaka da Siriya.
Piraministan na kasar Iraki ya bayyana cewa jami'an tsaron kasar sun sami gagarumar nasara wajen kare masu ziyarar arba'in a Karbala
Rahotanni daga kasar Iraki na nuni da cewa miliyoyin mabiya da masoya Ahlulbaiti (a.s) daga duk fadin duniya suna ci gaba da taruwa a birnin Karbala na kasar Irakin don gudanar da juyayin Arba'in na Imam Husain (a.s) don tunawa da cikar kwanaki 40 da kisan gillan da aka yi wa Imam Husainin da iyalai da magoya bayansa a shekara ta 61 bayan hijirar Ma'aiki (s).
Shugaban kasar Masar Abdul Fata Assisi ya ja kunnen shuwagabannin kasar Libya da su yi hattara kan shigowar yan ta'adda ta kungiyar Daesh wadanda aka kora daga kasashen Iraqi da siria zuwa kasar ta Libya
Tun da safiyar yau juma'a ne dai sojojin Irakin suka bude daga da gyauron 'yan Da'esh a garin na Ka'ima da ke yammacin gundumar Anbar.