Nov 15, 2017 06:37 UTC
  • Ibadi: Gwamnatin Tsakiya Za Ta Karbi Iko Da Dukkanin Iyakoki Daga Kurdawa

Pira ministan kasar ta Iraki Haydar Ibadi ya jaddada cewa za su karbi iyakokin ne ba tare da tashin hankali ko amfani da karfi ba.

Pira minista Haidar Ibadi ya kara da cewa; Bayan da gwamnatin yankin na Kurdawa ta ki amincewa da rubuta yarjejeniya da gwamnatin tsakiya, Bagadad za ta dauki matakin da ya dace dangane da iyakokin ba tare da ta  saurari shawarar da Arbil za ta yanke ba.

A ranar 16 ga watan Oktoba ne dai sojoji da kuma 'yan sandan Iraki suka kwace iko da birnin Karkuk wanda Kurdawan suke iko da shi, alhali akwai sabani akansa.

Kada kuri'ar raba gardama da Kurdawan suka yi domin ballewa daga Iraki, ya ba gwamnatin tsakiya ta Iraki damar ta shimfida ikonta akan yankunan da suke da sabani da Arbil.

Tags