Mar 12, 2019 05:49 UTC
  • Rohani: Alaka Tsakanin Iran Da Iraki, Alaka Ce Ta Dan Uwantaka Da Tarihi

Shugaban kasar Iran Dakta Hasan Rohani ya bayyana cewa alaka tsakanin kasashen Iran da Iraki, alaka ce da dan uwantaka dake da dadadden tarihi

A yayin da yake amsa tambayar manema labarai a birnin Bagdaza a marecen jiya Litinin, shugaba Rohani na jamhoriyar musulinci ta Iran ya bayyana jin dadinsa kan irin tarben da ya samu daga al'umma da mahukunta kasar Iraki, sannan ya ce alaka tsakanin kasashe biyu nada dadadden tarihi tare da dan uwantaka.

Yayin da yake ishara kan yadda al'ummar kasar Iran ta kasance tare al'ummar Iraki cikin mawuyaci hali da kuma bayar da duk wani taimakon da ya dace, shugaba Rohani ya ce samun tsaro da konciyar hankali na kasar Iraki na a matsayin bunkasar samun zaman lafiya da tsaro ga kasar Iran.

Shugaba Rohani ya tabbatar da cewa babu yadda za a samu tsaro da bunkasar yankin ba tare da taimakon kasashen Iran da Iraki ba, kuma a halin da ake ciki yanzu kasar Amurka ta kakabawa al'ummar Iran takunkumin zalinci da ya sabawa dokokin kwamitin tsaro na MDD domin karin matsin lamba da kuma shiga tsakanin kasashe aminai, domin haka, shugaba Rohani ya bukaci mahukuntan kasashen biyu da su kara karfafa alakar dan uwantakar dake tsakaninsu.

A karshe, Shugaba Rohani ya bayyana amincewarsa da yadda tawagar kasarsa ta samu karbuwa daga mahuntan kasar ta Iraki.

Tags