Pars Today
Koriya ta Arewa ta sake harba wani makami mai linzami da ya wuce ta sararin samaniyar kasar Japan, 'yan kwanaki bayan da Kwamitin Tsaron Majalisar Dinkin Duniya ya sanya mata wasu sabbin takunkumi.
Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya amince da gagarimin rinjaye da kudirin Amurka na tsananta wasu jerin sabbin takunkumai kan Koriya Ta Arewa bisa gwajin makamin nukiliyarta na baya baya nan.
John McCain wanda shi ne shugaban kwamitin Tsaro a majalisar dokokin Amurkan ya ce; Matukar Korea ta kai wa Amurka ko kawayenta hari,to za a shafe ta daga doron kasa.
Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel, ta ce tana da ra'ayin a samu mafita ta hanyar diflomatsiyya domin warware shirin nukiliya Koriya ta Arewa.
Amurka, a hukumance, ta bukaci a gudanar da zaman Kwamitin Tsaron Majalisar Dinkin Duniya don kada kuri'a kan daftarin kudurin da ta gabatar don kakabawa Koriya ta Arewa sabbin takunkumi saboda gwajin makaman nukiliya da ta yi kwanakin baya.
Kungiyar tsaro ta NATO ta bukaci ayi karin matsin lamba ga kasar korea ta arewa.
Babban sakatarin kungiyar tsaro ta NATO Jens stoltenberg ya yi Allah Wadai da gwajin makaman Nukiliya wanda kasar Koreya ta Arewa ta gudanar a jiya Lahadi
Sakatare Janar na kungiyar tsaron NATO yayi Allah wadai da gwajin makaman kare dangin da kasar Koriya ta arewa ta yi
Koriya ta Arewa ta sake gwajin wani makami nukiliya, wanda shi ne karo na shida, kamar yadda gwamnatin Japon ta tabbatar bayan jin girgiza kasa mai karfi maki 6,3 da sanyin safiyar yau Lahadi.
Shugaban kasar Koriya ta Arewa Kim Jong-Un ya sha alwashin ci gaba da harba makamai masu linzami ta kan Japon, tare da jadadda cewa harbin na ranar Talata data gabata tsomin tabi ne.