Koriya Ta Arewa Ta Sake Harba Wani Makami Mai Linzami
(last modified Fri, 15 Sep 2017 05:49:48 GMT )
Sep 15, 2017 05:49 UTC
  • Koriya Ta Arewa Ta Sake Harba Wani Makami Mai Linzami

Koriya ta Arewa ta sake harba wani makami mai linzami da ya wuce ta sararin samaniyar kasar Japan, 'yan kwanaki bayan da Kwamitin Tsaron Majalisar Dinkin Duniya ya sanya mata wasu sabbin takunkumi.

Kafafen watsa labaran kasar Japan sun ce a safiyar yau Juma'a ne Koriya ta arewa ta harba wannan makami mai linzami wanda aka ce ya tashi na tsawon kimanin mintuna 20 kafin ya fado cikin Tekun Pacific kimanin kilomita 2000 gabashin tsibirin Hokkaido.

Kasashen Japan da Koriya ta Kudu dai sun bayyana tsananin damuwarsu dangane da wannan gwajin makami da Koriya ta Arewan ta yi. Rahotanni sun ce gwamnatocin kasashen biyu sun kira zaman gaggawa na tsaro don tattauna lamarin, kamar yadda Amurka ma tace tana shirin kiran wani zama na gaggawa na Kwamitin tsaron MDD don tattaunawa kan lamarin.

A ranar Litinin din da ta gabata ce dai Majalisar Dinkin Duniya ta kakabawa Koriya ta Arewar wasu sabbin jerin takunkumi saboda gwaje-gwajen makaman nukiliya da ta yi a kwanakin baya. Koriyan dai ta ce tana yin wadannan gwaje-gwajen ne don kare kanta daga barazanar da Amurka take mata.