Mar 06, 2019 09:20 UTC
  • Amurka: Ko Korea Ta Yi Watsi Da Shirinta Na Makaman Nuklia

John Bolton, mai bawa shugaban kasar Amurka shawara kan al-amuran tsaro ya yi barazanar cewa dole ne Korea ta Arewa ta wargaza shirinta na makaman nukliya ko kuma Amurka ta kara dora mata wasu sabbin takunkuman tattalin arziki.

Bolton ya bayyanawa tashar talabijin ta Fox Business Network a jiya Talata kan cewa gwamnatin kasar Amurka tana son ta gano cewa da gaskiya ne Korea ta Arewa tana son wargaza makamanta na nukliya ko bahaka ba.

Wannan barazatar tana zuwa ne jim kadan bayan taron shuwagabannin kasashen biyu a birnin Hanoi na kasar Vetnam a karshen watan da ya gabata. Taron da aka kamala ba tare da sanya hannu a kan takarda ko guda ba.

Daga bayan dai shugaban Amurka Donal Trump ya fadawa taron yan jaridu kan cewa korea ta Arewa ta bukaci a dage mata dukkan takunkuman tattalin arzikin da ta dora mata, kafin da yi watsi da shiri nata.

Sai dai gwamnatin kasar Korea ta Arewa ta musanta hakan, inda ta bayyana cewa ta bukaci Amurka ta dauke mata wasu daga cikin takunkuman tattalin arzikin da ta dora mata ne.

 

 

Tags