Mar 05, 2019 17:54 UTC
  • Amurka Za Ta Aike Da Jami’an Diplomasiyya A Kasar Korea Ta Arewa

Sakataren harkokin wajen Amurka ne ya sanar da cewa; Nan da wani lokaci Amurkan za ta aike da jami’an diplomsiyya zuwa kasar Korea Ta Arewa domin cigaba da tattaunawa

Sakataren  harkokin wajen kasar ta Amurka Mike Pempeo ya ce; Nan da wasu makwanni masu zuwa ne Amurka za ta aike da tawagar.

Pempeo ya kara da cewa; Abin da su ka sanya a gaba shi ne nemo abubuwan da su ka yi tarayya akansu.

Sau biyu dai aka yi ganawa a tsakanin shugabannin kasashen Amurka da na Korea Ta Arewa, da zummar gano zaren yadda za a kwance damarar yakin Nukiliya a yankin Korea.

Tags