Nov 16, 2017 05:42
Ministan harkokin wajen kasar Labanon, Gebran Bassil, ya bayyana shakkunsa dangane da halin da firayi ministan kasar Sa'ad Hariri yake ciki a kasar Saudiyya yana mai cewa ci gaba da zaman Haririn a Saudiyya ba tare da dawowa gida ba wani lamari ne mai ban mamaki da tada hankali da ke nuni da cewa lalle ba dai lafiya ba.