Labanon : Bassil, Ba Zai Halarci Taron Kasashen Larabawa Ba Kan Iran
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i25551-labanon_bassil_ba_zai_halarci_taron_kasashen_larabawa_ba_kan_iran
Ministan harkokin waje na kasar Labanon, Gebrane Bassil, ba zai halarci taron kungiyar kasashen larabawa ba da Saudiyya ta kira kan Iran.
(last modified 2019-04-27T09:55:10+00:00 )
Nov 19, 2017 06:35 UTC
  • Labanon : Bassil, Ba Zai Halarci Taron Kasashen Larabawa Ba Kan Iran

Ministan harkokin waje na kasar Labanon, Gebrane Bassil, ba zai halarci taron kungiyar kasashen larabawa ba da Saudiyya ta kira kan Iran.

Labanon dai ta yanke shawara cewa wakilinta na dindin-din a kungiyar ne zai halarci taron na yau a birnin Alkahira.

Saudiyya ce dai ta bukaci taron bisa batun makami mai linzamin nan da 'yan gwagwarmaya na Houtsi a Yeman da suka cilla wanda Saudiyyar ta ce ta cafke a kusa da birnin Ryad a ranar 4 ga watan nan.

Hankulan 'yan siyasa dai a Labanon ya rabu matuka a cacar baki ta tsakanin kasashen Saudiyya da Iran masu fada a ji a yankin.