Mar 14, 2019 07:40 UTC
  • Amurka Ta Wanke Bn Salman Daga Kisan Khashoggi

Cikin wani rahoto da gwamnatin Amurka ta fitar kan hakkokin kare hakin bil-adama na shekara-shekara, ba a yi ishara kan rawar da bn salman ya taka a kisan Jamal Khashoggi ba.

Kamfanin dillancin labaran Fars ya habarta cewa a jiya laraba ce hukumar kare hakin bil-adama ta kasar Amurka ta fitar da rahoton shekara-shekara ba tare da ta yi ishara da yarima mai jiran gado na  kasar Saudiya Muhamad bn Salam ba kan kisan gillar da aka yiwa shahararren dan jaridan nan wanda ya yi fice a sukan siyasar saudiya jamal Khashoggi

Rashin ambato sunan bn salaman kan kisan Khashoggi na zuwa a yayin da ma'aikatar leken asirin Amurka ta ce ta yi imanin cewa bn salman ne da kansa ya bayar da umarnin kisan jamal Khashoggi a karamin ofishin jakadancin kasar Saudiya dake birnin Istambul na kasar Turkiya.

A yayin zaman, saktaren harakokin wajen Amurka Mike Pompeo ya zarki kasashen Iran da China da Nicaragua dake a matsayin manyan kasashen dake adawa da manufofin kasar Amurka da take hakin bil-adama.

Tags