-
Sayyid Nasrallah: Sahyoniyawa Za Su Kwashi Kashinsu A Hannu Matukar Suka Kaddamar Da Yaki Kan Hizbullah
Oct 01, 2017 10:23Shugaban kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon Sayyid Hasan Nasrallah ya ja kunnen haramtacciyar kasar Isra'ila da cewa za su debi kashinsu a hannun matukar gigi ya debe su suka kaddamar da yaki a kan kungiyar Hizbullah yana mai kiran yahudawan da suka yiyo hijira zuwa "Isra'ila" da su gaggauta komawa inda suka fito.
-
Wata Kotun Soji A Kasar Lebanon Ta Yanke Hukuncin Kisa Kan Sheikh Ahmad Asir
Sep 29, 2017 05:08Wata kotun soji a kasar Lebanon ta yanke hukuncin kisa kan malamin yan ta'adda Sheikh Ahmad Asir a jiya Alhamis saboda samunsa da laifin kisan sojojin kasar
-
Sayyid Nasrallah: Za Mu Gutsure Hannun Duk Wanda Ya So Wuce Gona Da Iri Kan Labanon
Aug 31, 2017 17:56Shugaban kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon Sayyid Hasan Nasrallah ya ja kunnen masu son wuce gona da iri kan kasar Labanon da cewa za su debi kashinsu a hannu don kuwa lokacin wuce gona da irin ya wuce.
-
Sayyid Nasrallah: 'Yan Da'esh Ba Su Da Wata Mafita Face Mika Kai
Aug 29, 2017 05:40Shugaban kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon, Sayyid Hasan Nasrallah ya bayyana cewar 'yan kungiyar ta'addancin nan ta Da'esh da aka fatattaka daga kan iyakokin Siriya da Labanon ba su da wata mafita face kawai su mika kansu ga dakarun gwagwarmaya.
-
Nasrullah: Dakarun Lebanon, Syria Gami Da Hizbullah Suna Samun Nasara A Kan ISIS
Aug 25, 2017 05:17Babban sakataren kungiyar Hizbullah Sayyid Hassan nasrullah ya bayyana cewa, a ci gaba da fatattakar 'yan ta'addan ISIS da dukkanin bangarori na dakarun Lebanon, da kuma sojojin Syria tare da mayakan Hizbullah ke yi, ana samun gagarumar nasara.
-
Sojojin Labanon Sun Kaddamar Da Hare-Haren Korar 'Yan Kungiyar Da'esh Daga Kasar
Aug 19, 2017 16:35Babban hafsan sojojin kasar Labanon Sojojin Janar Joseph Aoun ya bayyana cewar sojojin kasar sun kaddamar da hare-haren zuwa sansanonin 'yan kungiyar ta'addancin nan ta Da'esh da suke gabashin kasar da nufin fatattakansu daga yankunan kasar da suke rike da su.
-
Sayyid Nasrallah Ya Ja Kunnen 'Yan Da'esh Da Su Bar Labanon Tun Lokaci Bai Kure Musu Ba
Aug 05, 2017 10:24Shugaban kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon Sayyid Hasan Nasrallah ya jinjinawa dakarun kungiyar saboda nasarar da suka samu na fatattakan 'yan kungiyar ta'addancin nan ta Jabhatun Nusra daga kasar yana mai jan kunnen 'yan kungiyar Da'esh da su yi kiyamul laili wa kansu su bar kasar tun lokaci bai kure musu ba.
-
Dakarun Hizbullah 5 Da Jabhatun Nusra Ta Sace Sun Dawo Gida
Aug 04, 2017 10:38Rahotanni daga kasar Labanon sun bayyana cewa ana ci gab da gudanar da bukukuwan farin ciki don maraba da dakarun kungiyar Hizbullah na kasar su 5 da suka dawo gida bayan sama da shekara guda a hannun 'yan kungiyar ta'addancin nan ta Jabhatun Nusra' da ke da alaka da kungiyar Al-Qa'ida.
-
An Fara Musayen Fursunoni Tsakanin Hizbullah Da Jabhatun Nusra
Aug 02, 2017 11:05Rahotanni daga kasar Labanon sun bayyana cewar an fara aiwatar da mataki na biyu na yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon din da kungiyar ta’addancin nan ta Jabhatun Nusrah, inda ‘yan ta’addan suka sako wasu dakarun kungiyar Hizbullah din su uku da suka kama a bangare guda kuma gwamnatin Labanon din ta sako ‘yan kungiyar su uku da take tsare da su.
-
An Cimma Yarjejeniyar Tsagaita Wuta Tsakanin Hizbullah Da 'Yan Ta'adda
Jul 27, 2017 12:17Rahotanni daga kasar Lebanon sun sheda cewa an cimma yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin dakarun Hizbullah da kuma 'yan ta'addan takfiriyyah na Jabhat Nusra.