Dakarun Hizbullah 5 Da Jabhatun Nusra Ta Sace Sun Dawo Gida
(last modified Fri, 04 Aug 2017 10:38:25 GMT )
Aug 04, 2017 10:38 UTC
  • Dakarun Hizbullah 5 Da Jabhatun Nusra Ta Sace Sun Dawo Gida

Rahotanni daga kasar Labanon sun bayyana cewa ana ci gab da gudanar da bukukuwan farin ciki don maraba da dakarun kungiyar Hizbullah na kasar su 5 da suka dawo gida bayan sama da shekara guda a hannun 'yan kungiyar ta'addancin nan ta Jabhatun Nusra' da ke da alaka da kungiyar Al-Qa'ida.

A daren jiya ne dai dakarun kungiyar Hizbullah din su biyar wato Hasan Nazihi Taha, Muhammad Mahdi Hani Shu'aib, Musa Muhammad Kurani, Muhammad Jawad Ali Yasin da Ahmad Mazhar suka iso kasar Labanon daga kasar Siriya dubun dubatan al'umma da suka hada da wasu jami'an kungiyar Hizbullah, 'yan majalisar kasar Labanon din da sauran 'yan siyasar kasar suka yi musu gagarumar tarba.

Su dai wadannan dakarun su biyar sun dawo gida din ne cikin musayen fursunoni da ya gudana tsakanin kungiyar Hizbullah din da 'yan kungiyar Jabhatun Nusra din wadanda suka kama su a kasar Syria.

A daren yau ne dai ake sa ran shugaban kungiyar Hizbullah din Sayyid Hasan Nasrullah zai gabatar da jawabi dangane da wannan lamarin da sauran batutuwan da suka shafin gumurzun da kungiyar Hizbullah din ta yi da 'yan kungiyar Jabhatun Nusra' din a yankin Arsal na kasar inda suka fatattake su daga wajen bayan kimanin shekaru uku da mamaye wajen da suka yi.