Pars Today
Sojojin yahudawa sahayoniya sun kashe falasdinawa akalla 55 a zirin Gaza, a zanga zanga da falastinawan ke yi kan mayar da Kudus babban birnin haramtacciyar kasar Isra'ila.
Mafi yawan kasashen yammacin turai sun ki karba goron gayyata domin halartar bikin bude ofishin jakadancin Amurka a birnin Quds mai alfarma.
Gwamnatin kasar Rasha ta gargadi kasar Amurka kan anniyarta na maida ofishin jakadancinta daga Telaviv zuwa birnin Quds a kasar Palasdinu da aka mamaye.
Daga lokacin da Shugaba Trump na Amurka ya bayyana Qudus a matsayin hedkwatar Isra'ila zuwa yanzu Palastinawa 94 ne suka yi shahada sanakamakon harbinsu da jami'an tsaron Sahayuna suka yi.
Taron kasashen larabawa da ya gudana a birnin Dammam na kasar Saudiyya, ya jaddada yin watsi da matakin shugaba Donald Trump na Amurka na ayyana Qudus a matsayin babban birnin mahukuntan yahudawan mamaya na Isra'ila.
Shugaban Majalisar Dokokin kasar Moroko ya bayyana matakan wuce gona da iri da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila take dauka a kan al'ummar Palasdinu a matsayin take dokokin kasa da kasa.
Shugaban kungiyar Hamas Isma'ila Haniyyah da yake magana akan ranar tunawa da hakkin komawar Palasdinawa zuwa gidajensu ya ce; Abin da ya faru ayau makomar koamawa ce zuwa dukkanin palasdinu
An bude babbar gasar kur'ani ta duniya a kasar Masar tare da halartar daruruwan makaranta daga kasashen duniya 50.
Sojojin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila sun kai farmaki kan wata makarantar Palasdinawa da ke yammacin birnin Qudus, inda suka tarwatsa dalibai tare da jikkata da dama daga cikinsu.
An kammala zaman taron yini uku da aka gudanar a kasar Masar, kan samo hanyoyin yaki da tsatsauran ra'ayi da kuma dakile yaduwarsa a cikin kasashen musulmi.