Larabawa Sun Jaddada Yin Watsi Da Matakin Amurka Kan Qudus
Taron kasashen larabawa da ya gudana a birnin Dammam na kasar Saudiyya, ya jaddada yin watsi da matakin shugaba Donald Trump na Amurka na ayyana Qudus a matsayin babban birnin mahukuntan yahudawan mamaya na Isra'ila.
A jawabinsa a taron, Sarki Salmane, ya ayyana taron karo na 29 da '' taron Qudus'' domin a cewarsa duniya ta san Palasdinu da al'ummarta na daga cikin ababen da kasashen larabawa suka damu dasu, tare da jaddada gabashin Qudus a matsayin babban birnin Palasdinu.
Sarkin na Saudiyya ya kuma sanar da talafin Dalar Amurka Miliyan 150, domin karfafa wa ayyukan kyautata Musulunci a yankin gabashin Qudus da 'yan sahayoniya suka mamaye.
Wannan dai tamakar wata alama ce ta wanke kwabar da matashin yarima mai jiran gado na Saudiyar ya yi kwanan baya na cewa ''hakkin Isra'ila ne ta mallaki kasarta''
A cikin jawabin nasa sarki Salman ya tabo batun ta'addanci da kuma sake bayyana Iran a matsayin mai shishigi a cikin harkokin cikin gidan kasashen Larabawa, saidai bai tabo batun yakin Siriya ba da kuma na sabanin dake tsakanin kasarsa da Qatar ba, saidai gabanin taron Saudiyyar ta nuna goyan baya ga hare haren baya bayan nan da kasashen Amurka, Birtaniya da kuma Faransa suka kai a Siriyar.
A nasa bangare sakatare janar na kungiyar kasashen larabawan, Ahmed Aboul Gheit, ya yi kira ga kasashe 22 mambobin kungiyar dasu dukufa wajen farfado da shirin magance rikicin kasar Siriya ta hanyar siyasa.