Mar 11, 2019 10:35 UTC
  • Harin Kawancen Saudiyya Ya Kashe Mutum 21 A Yemen

Akalla Mata 20 ne da karamin yaro guda suka rasa rayukansu sakamakon ruwan bama-bamai da jiragen yakin kawancen saudiya suka yi a kasar Yemen

Kamfanin dillancin labaran Irna ya habarta cewa harin da jiragen yakin saudiya suka kai a Lardin Talanil-Kashir dake jihar Hajjah a jiya Lahari, harwa yau yayin sanadiyar rusa gidajen fararen mazauna yankin da dama.

Rahoton ya ce jiragen yakin kawancen saudiyan sun kai farmaki kan wasu jerin motocin kai agaji da na daukan marassa lafiya, lamarin ya kawo tsaiko na kaiwa marassa lafiya dauki a yankin.

A ranar juma'ar da ta gabata ma, jiragen yakin kawancen saudiyar sun kai irin wannan hari a garin Kashir, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwa da kuma jikkatar mutum 12 'yan gida guda.

Tun a watan Maris din 2015 ne kasar Saudiya tare da hadaddiyar daurar larabawa bisa cikekken goyon bayan kasar Amurka suka fara kai harin wuce gona da iri kan kasar Yemen tare da killace kasar ta sama, ruwa da kuma kasa.

Bayan kwashe kusan shekaru hudu, babu wani abu da masarautar saudiya tare kawayenta suka cimma a kasar ta yemen, face kisan dubun dubatan fararen hula da rusa gine-ginen kasar, sakamakon juriya da kuma gwagwarmaya na al'ummar kasar ta Yemen.

Tags