Yemen: An Kashe "Yan Koren Saudiyya 20 A Kan Iyaka
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i34982-yemen_an_kashe_yan_koren_saudiyya_20_a_kan_iyaka
Sojojin Yemen da su ka yi bata-kashi da 'yan koren Saudiyya sun kashe 20 daga cikinsu
(last modified 2019-01-28T07:46:16+00:00 )
Jan 28, 2019 07:46 UTC
  • Yemen: An Kashe

Sojojin Yemen da su ka yi bata-kashi da 'yan koren Saudiyya sun kashe 20 daga cikinsu

Tashar Talbijin din 'al'alam' ta ambato majiyar sojan Yemen suna cewa; Da marecen ranar Asabar an yi taho mu gama a tsakanin sojojin Yemen da 'yan koren Saudiyya a gundumar Najaran dake kudancin Saudiyya, tare da kashe ashirin daga cikinsu da kuma jikkata wasu 30.

A wani gefen, sojojin na Kasar Yemen sun harba makamai biyu masu linzami samfurin Zilzal 1 akan sansanin 'yan koren Saudiyyar da ke Sahara'ul Baqi'a a gundumar Najran

Kawo ya zuwa yanzu babu cikakken rahoto akan adadin asarar da harin ya haddasa

Saudiyya ta shelanta yaki akan Yemen a 2015 bisa cikakken goyon bayan Amurka. Ya zuwa yanzu mutanen da kawancen yakin na Saudiyya ya kashe sun kai 14,000.