Apr 20, 2017 11:23
Wasu majiyoyin labarai sun bayyana cewar akwai yiyuwar kwamitin da shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari ya kafa don binciko kimanin Naira biliyan 13 da hukumar EFCC mai fada da ta'annuti ga tattalin arzikin kasar ta gano a Lagos ya gayyaci tsohon shugaban kasar Goodluck Jonathan, gwamnan babban bankin kasar Godwin Emefiele da kuma shugaban EFCC din don neman karin bayani daga wajensu.