-
Sayyid Nasrallah: Za Mu Gutsure Hannun Duk Wanda Ya So Wuce Gona Da Iri Kan Labanon
Aug 31, 2017 17:56Shugaban kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon Sayyid Hasan Nasrallah ya ja kunnen masu son wuce gona da iri kan kasar Labanon da cewa za su debi kashinsu a hannu don kuwa lokacin wuce gona da irin ya wuce.
-
Sayyid Nasrallah: 'Yan Da'esh Ba Su Da Wata Mafita Face Mika Kai
Aug 29, 2017 05:40Shugaban kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon, Sayyid Hasan Nasrallah ya bayyana cewar 'yan kungiyar ta'addancin nan ta Da'esh da aka fatattaka daga kan iyakokin Siriya da Labanon ba su da wata mafita face kawai su mika kansu ga dakarun gwagwarmaya.
-
Sayyid Nasrallah: Isra'ila Tana Tsoron Sake Kai Hari Labanon Saboda Karfin Hizbullah
Aug 13, 2017 17:02Shugaban kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon Sayyid Hasan Nasrallah ya bayyana cewar zamanin barazanar 'Isra'ila' ya wuce kuma ba zai dawo ba har abada, don kuwa ta san cewa karfin kungiyar Hizbullah ya karu sama da na lokacin yakin shekara ta 2006.
-
Sayyid Nasrallah Ya Ja Kunnen 'Yan Da'esh Da Su Bar Labanon Tun Lokaci Bai Kure Musu Ba
Aug 05, 2017 10:24Shugaban kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon Sayyid Hasan Nasrallah ya jinjinawa dakarun kungiyar saboda nasarar da suka samu na fatattakan 'yan kungiyar ta'addancin nan ta Jabhatun Nusra daga kasar yana mai jan kunnen 'yan kungiyar Da'esh da su yi kiyamul laili wa kansu su bar kasar tun lokaci bai kure musu ba.
-
Sayyid Nasrallah: Hizbullah Sun Kwato Kusan Dukkanin Yankunan Labanon Dake Hannun Jabhatun Nusra
Jul 27, 2017 05:26Shugaban kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon Sayyid Hasan Nasrallah ya bayyana cewar dakarun kungiyar sun kusa kwato dukkanin yankunan kasar Labanon da 'yan kungiyar ta'addancin nan ta Jabhatun Nusra suke rike da su tsawon shekaru, yana mai jinjinawa irin namijin kokarin da dakarun kungiyar da sojojin Labanon suka yi wajen cimma wannan nasarar.
-
S. Nasrallah: Saudiyya Ta Girmama Trump Ne Don Samun Goyon Bayan Yakar Iran
May 25, 2017 18:08Shugaban kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon Sayyid Hasan Nasrallah ya bayyana taron da Saudiyya ta shirya don maraba da shugaban kasar Amurka Donald Trump a matsayin wani kokari na girmama Trump din da kada kugen yaki a kan kasar Iran da sauran kungiyoyin gwagwarmaya yana mai cewa hakan babu abin da zai kara musu face tsayin daka kan tafarkin da suke kai.
-
Sayyid Nasrallah: Wajibi Ne A Hukunta Saudiyya Da Amurka Saboda Kirkiro Da'esh
Feb 16, 2017 18:04Shugaban kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon Sayyid Hasan Nasrallah ya bayyana cewar wajibi ne a hukunta gwamnatocin Saudiyya da Amurka saboda kirkiro kungiyar ta'addancin nan ta Da'esh (ISIS) da kuma goyon bayanta.
-
Sayyid Nasrallah: Ba Ma Cikin Damuwa Don Kuwa Sabon Shugaban Amurka Wawa Ne
Feb 12, 2017 17:14Shugaban kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon Sayyid Hasan Nasrallah ya gode wa shugaban kasar Amurka Donald Trump sakamakon yadda ya bayyanar da hakikanin yanayin Amurka wa duniya, yana mai cewa ba sa cikin wata damuwa don kuwa wawa ne ke mulkin Amurkan.
-
Sayyid Nasrullah: Tuhumar Musulunci Da Ta'addanci Makircin Yammacin Turai Ne
Dec 23, 2016 18:03Babban sakataren kungiyar Hizbullah a kasar Lebanon Sayyid Hassan Nasrullah, ya bayyana cewa kiran kungiyoyin 'yan ta'adda da sunaye masu kama da muslunci irin su daular muslunci da suke kiran (Daesh) ISIS, ko ta'addancin mulsunci (Islamic terrorism) da kalmamomi masu kama da haka, duk yunkuri ne na yakar muslunci da rusa shi a fakaice.
-
Hasan Nasrullahi Ya Ce: Mutanen Da Suka Kunna Wutar Rikici A Lebanon Su Zasu Afka Ciki
Dec 10, 2016 05:44Babban sakataren kungiyar Hizbullahi ta kasar Lebanon ya bayyana cewa: Mutanen da suke kokarin kunna wutar rikici da tashe-tashen hankula a kasar Lebanon sune farkon wadanda zasu afka ciki.