Pars Today
Shugaban na kasar Iran da ya gana da takwaransa na kasar Zimbabwe Robert Mogabe, ya ce; Kasashen biyu suna da dama mai yawa da su iya bunkasa alakarsu a cikinsu.
Piraministan Kasar Senegal ya sanar da cewa gamayar jam'iyun dake marawa Shugaban kasar baya sun zamu nasara a zaben 'yan majalisar da aka gudanar lahadin da ta gabata.
A Senegal, yau Lahadi ne al'ummar kasar da suka tantanci kada kuri'a ke zaben 'yan majalisar dokoki, wanda ke zamen zakaran gwajin dafin zaben shugaban kasar na shekara 2019 dake tafe.
Sabani na kara tsanani tsakanin gwamnatin da jam'iyun adawa a yayin da ake shirye-shiryen gudanar da zaben 'yan majalisar dokoki a kasar Senegal.
A Senegal, a yayin da zaben 'yan majalisar dokokin kasar ke kara karatowa, ana ci gaba da tada jijiyoyin wuya akan sabon tsarin da gwamnatin kasar ta bijiro da shi kan zaben na ranar lahadi mai zuwa.
A Senegal an bude bincike domin gano musababin hadarin da ya yi sanadin mutuwar mutane takwas a wani filin kwallon kafa dake Dakar babban birnin Kasar a ranar Asabar data gabata.
Mutuwar mutanen ta zo ne a daidai lokacin da ake kallon wasan karshe na zama zakaran kwallon kafa a kasar.
A Senegal, shekara guda bayan kaddamar da shirin nan na hana barace-barace na yara almajirai, kungiyoyi masu zamen kansu sun ce ba'a cimma gurin da ake so ba.
A kasar Senegal an bude yakin neman zaben 'yan majalisar dokokin kasar da za'a gudanarwa a ranar 30 ga watan Yulin nan da muke ciki.
An fara gudanar da wasu shirye-shirye na ranar Quds a kasar Senegal, da suka hada da tarukan karawa juna sani da sauransu.