Pars Today
Shugaban kasar Syria Bashar Assad ya bayyana cewa; yada rarraba tsakanin al'umma da kuma yada tsattsauran ra'ayi da sunan addini, su ne manyan makaman da makiya suke yin amfani da su a halin yanzu domin raunana al'ummar musulmi a duniya.
Mataimakin bababn jami'in sojin kasar Rasha da ke kula da ayyukan soji a wajen kasar Janar Virtor Pozen ya bayyana kungiyiyoyin da ke shiga cikin Syria da sunan ayyukan agaji, su ne suka shirya wasan kwaikwayon kai hari da makamai masu guba.
Tashar talabijin din Sky News ta ba da labarin cewa;Jiragen yaki na kawancan da Amurka take jagoranta sun yi shawagi a kan iyakar Iraki da Syria
Jim kadan bayan da Rashan ta hau kujerar na-ki akan daftarin kudurin da Amurkan ta gabatar, Ita ma Amurkan da kawayenta na turai sun yi watsi da kudurin Moscow
Gwamnatin Siriya ta musanta yin amfani da makamai masu guba a gabashin yankin Ghouta dake Damascus, kuma ta ce zargin da aka yi mata babu kamshin gaskiya.
Majiyar Sojan Syria ta ce; sojojin kasar sun harba na'urorin kakkabo makamai masu linzami inda su ka yi nasarar harbo guda 8 a saman filin saukar jiragen sama na soja da ke Tifur
Rahotanni daga kasar Syria sun ambato cewa, kimanin mutane 6 suka rasa rayukansu a jiya, biyo bayan harba makaman roka da 'yan ta'adda na kungiyar Jaish Islam suka yi daga unguwar Doma da ke gabashin Ghouta zuwa birnin Damascus.
Sabanin mahanga tsakanin shugaban kasar Amurka da fira ministan gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila kan kasar Siriya yana neman yin kamari.
Sojojin kasar Syria sun sanar da gano kurkukun ne a garin Zamalka da ke yankin Ghuta wanda kuma kungiyar 'yan ta'addar "Failaq-Rahman' take tafiyar da shi.
Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya bayyana cewa Amurka za ta yanke shawara game da janye sojojinta a yankin gabas ta tsakiya ko kuma akasin haka nan bada dadewa ba.