Trump Na Tunanin Janye Sojojin Amurka Daga Siriya
Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya bayyana cewa Amurka za ta yanke shawara game da janye sojojinta a yankin gabas ta tsakiya ko kuma akasin haka nan bada dadewa ba.
Trump yana mai cewa matakin soja da Amurka ta dauka cikin shekaru 10 da suka shude a yankin gabas ta tsakiya na lakume makudan kudade amma ba tare da samar da wani amfani ba.
A wannan rana kuma, Trump ya gana da shugaban Estonia Kersti Kaljulaid, da shugaban Latvia Raimonds Vējonis da shugaban Lithuania Dalia Grybauskaitė dake ziyara a kasar.
Yayin taron manema labaru na hadin gwiwa da shugabannin suka yi, Trump ya ce, burin matakin soja da Amurka ta dauka a Sham shi ne murkushe kungiyar IS, kuma a yanzu ta kusan cimma wannan buri