-
Siriya : Faransa Ta Sanya Takunkumi Kan Wasu Kamfanoni Da Jami'ai 25
Jan 23, 2018 07:47Kasar Faransa ta sanar da kakaba takunkumi kan wasu Cibiyoyi da jami'ai su 25 kan zargin taimakawa shirin Siriya na sarafawa da kuma kera makamai masu guba.
-
Kasar Iran Ta Ce: Amurka Da Kawayenta Suna Ci Gaba Da Kulla Sabbin Makirci Kan Kasar Siriya
Jan 21, 2018 03:48Shugaban cibiyar gudanar da tsare-tsare kan harkokin siyasar wajen Jamhuriyar Musulunci ta Iran ya ce; Kasar Amurka da kawayenta suna ci gaba da kulla wasu sabbin makirce-makirce kan kasar Siriya.
-
Majalisar Dinkin Duniya Ta Bayyana Damuwarta Kan Rikicin Yankin Afrin Na Kasar Siriya
Jan 21, 2018 03:40Majalisar Dinkin Duniya ta nuna damuwarta kan rikicin da ya kunno kai tsakanin sojojin Turkiyya da mayakan kurdawan kasar Siriya a yankin Afrin da ke arewacin kasar ta Siriya.
-
Kimanin 'Yan Gudun Hijra Dubu 31 Ne Suka Koma Iraki Daga Kasashen Turkiya Da Siriya
Jan 18, 2018 08:15Ma'aikatar 'yan gudun hijra ta kasar Iraki ta sanar da komawar 'yan kasar ta kimanin dubu 31 zuwa 'yan kunansu da aka tsarkake daga kasashen Turkiya da Siriya
-
Sojojin Gwamnatin Siriya Sun Halaka 'Yan Ta'adda Fiye Da 70 A Yankin Arewa Maso Yammacin Kasar
Jan 13, 2018 03:02A wani samame da sojojin gwamnatin Siriya suka kai kauyen Adshan da ke lardin Idlib a shiyar arewa maso yammacin kasar sun yi nasarar kashe 'yan ta'adda fiye da 70.
-
An Sami Karuwar Masu Yawon Bude Ido A Kasar Syria A 2017
Jan 11, 2018 07:44Ma'aikatar yawon bude-ido ta kasar Syria ta sanar da cewa fiye da mutane miliyan daya suka ziyarci kasar a 2017
-
Sojojin Siriya Sun Kwato Filin Jirgin Saman Abul Zuhur Da Ke Idlib
Jan 11, 2018 02:17Rahotanni daga kasar Siirya sun bayyana cewar sojojin kasar sun sami nasarar kwato filin jirgin saman soji na Abul Zuhr da ke garin Idlib daga hannun kungiyar ta'addancin nan ta Jabhatun Nusra.
-
Sojojin Siriya Sun Ce Sun Harbe Wani Jirgin Yakin 'Isra'ila' Da Ke Shirin Kawo Hari Kasar
Jan 09, 2018 07:53Rundunar sojin kasar Siriya ta sanar da cewa makamai masu linzamin kasar masu kakkabo jiragen yaki sun harbe wani jirgin yakin haramtacciyar kasar Isra'ila bugu da kari kan kakkabo wasu makamai masu linzamin da sahyoniyawan suka harbo cikin kasar ta Siriya.
-
Syria: Sojojin Sun Bude Kai Hare-hare Akan Rundunar "Jaishul-Islam"
Jan 01, 2018 15:25Sojojin Syria sun fara kai harin ne a yankunan Huzrama da Zuraify da suke gabacin da birnin Damashka, da mayakan "JaishulIslam' suke da sansani
-
Rasha Ta Yi Watsi Da Ikararin Trump Na Cin Nasara A Siriya
Dec 31, 2017 15:49Shugaban kwamitin Tsaron kasa na Majalisar kasar Rasha ya ce nasarar da shugaban kasar Amurka ke da'awar yi a kasar Siriya ba shi da kamshin gaskiya.