Pars Today
An kammala taron koli na kungiyar tarayya Afrika da Turai karo na biyar a birnin Abidjan na kasar Ivory Coast inda shugabanni nahiyoyin biyu suka kudirin anniyar yaki da kwararar bakin haure ba bisa ka'ida ba, da kuma kalubalen dake cikinsa kamar cinikin bakin haure a Libiya.
Shugabannin tarayyar Afirka a kuma na turai da MDD sun cimma yarjejniyar fitar da bakin hauren cikin gaggawa daga Libya
Kotun hukunta manyan laifuffuka ta duniya da ke birnin Hague ta dakatar da shari’ar da ake yi wa Slobodan Praljak da ake zargi da aikata laifukan yaki a Bosniya bayan ya kwankwadi guba a gaban kotun.
Kasashen Faransa, Nijar da Chadi, da MDD da kungiyoyin EU da AU zasu gudanaar da wani taron gaggawa kan batun bautar da bakin haure a Libiya a daura da taron koli na tarayya Turai da AFrika a birnin Abdijan na kasar Ivory Coast.
Kwamishinan ayyukan noma da kuma raya karkara na tarayyar Turai Mr Phil Hogan ya bayyana cewa ba wata kasa a cikin tarayyar turai da take da tunanin dorawa Iran takunkumi idan Amurka ta yi watsi da yerjejeniyar da ta kulla da ita.
Shugaban gwamnatin Spaniya, Mariano Rajoy, ya nemi majalisar dattijan kasar ta bada izinin tsige shugaban 'yan a ware na yankin Kataloniya.
Gungun kasashe G7 mafiya karfin tattalin arziki a duniya da mayan kamfanonin internet sun cimma matsaya kan toshe duk wata farfaganda dake da alaka da yada ta'addanci.
Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel da shugaban kasar Faransa Emanuel, sun jadadda goyan bayansu ga gwamnatin Madrid kan rikicin yankin Cataloniya, a yayin da takwaransu na Biegium ke kiran a kai zuciya nesa.
Hukumar hijira ta kasa da kasa ta sanar da raguwar masu son zuwa ci-rani zuwa nahiyar turai.
Bincike ya tabbatar da cewa: Kasashen Yammacin Turai sun fi cutuwa daga takunkumin da suka kakaba kan kasar Rasha.